Tawagar kasar Iran a gasar fasahar kumfuta ta IOI 2024 ta zo na 9TH a cikin kasashe 96 da suka halarci gasar fasahar kumfuta karako na 36Th wanda kuma ake kira ‘36th International Olympiad in Informatics (IOI 2024) a birnin Eskandariya na kasar Masar daga ranar 1-8 ga watan satumban da muke ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tawagar kasar Iran bata sami damar zuwa kasar Masar ba, saboda matsalolin shige da fice, ammam ta shiga kasar ta yanar gizo, inda ta samu lambobin yabo wadanda suka hada da Zinari, Azurfa da kuma tagulla.
Labarin ya kara da cewa Amir Ali Asgari ya sami lambar yabo ta zinari, Amir Hossein Farkhondehfar da kuma Amir Reza Dorosti ko wannensu ya sami lambobin yabo na azurfa sai kuma Parsa Farajpour wanda ya sami lambar tagulla.
Kungiyar Arab Academy for Science, Technology and Maritime Transport (AASTMT) ne take daukar nauyin wannan gasar. Kuma shi ne gasar Olympiad mafi muhimman a cikin gasanni Olumpiad 5 na ilmi da ake gudanarwa a duniya. Kasashen China, Amurka da kuma Poland ne suka zo na farko, na biyu da na uku a gasar na bana.