An kaddamar da cibiyar kirkirarren Fasaha’ wa (AI) a wani mataki na karfafa ilmin fgasahar zamani mai zurfi a kasar Iran. Kuma wannan wani sabon mataki ne na bunkasa ilmin fasahar zamani mai zurfi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa mukaddashin shugaban kasa Mohammad Mukhbir ne ya jagoranci kaddamar da wannan cibiyar a nan birnin Tehran.
A jawabinsa a taron kaddamar da cibiyar ta bunkasa (AI), mukaddashin shugaban kasa Mohammad Mukhbir ya bayyana cewa marigayi shugaba Ra’isi ne ya kirkiro tunanin kafa cibiyar a shekara ta 2023, sannan ya bada duk abinda ake bukata don tabbatar hakan.
Labarin ya kara da cewa cibiyar tana aiki da dukkanin ma’aikatun gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansa wadanda abin ya shafa a duk fadir kasar don cimma wannan manufar.
Ana sanar cibiyar zata bunkasa fasahar kwararrun kasar Iran, don kirkiro abubuwa masu amfani don ci gaban kasar da kuma kyautata tattalin arzakin kasar.