Wakili kuma jakadan JMI a MDD dake birnin NewYork ya mikawa kwamitin tsaro na majalisar wasika inda a ciki yake maidawa kasashen larabawa martini kan tuhumar kasar da kwace iko da mallakar tsibirai guda uku da suke cikin tekun Farisa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Sa’eed Iravani jakadan Iran a MDD yana fadar haka ya kuma kara da cewa tuhumar mamayar da kasashen Larabawa suke wa JMI kan tsibiran Abu Musa, Tumbe Bozorg da Tumbe kucek ya samawa kyautata makobtaka tsakanin Iran da wadannan kasashen larabawa, sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa, wadanda suka tabbatar da cewa wadanan tsibiran mallakin kasar Iran ne tun shekaru da dadewa.
A wani bangare kuma a cikin wasikar, Jakadan ya bayyana cewa tekun farisa sunane wanda yankin ruwan da tsakanin kasashen Larabawa da Iran yake da shi tun shekaru aro aro, don haka JMI tana allawadai da canza sunan ruwan zuwa tekun larabawa.