Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bada sanarwan cewa an nada jakadan kasar na musamman mai kula da al-amuran kasar Siriya a dai dai lokacinda ake samun sauye-sauyen masu muhimmanci a yankin Asiya ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Esma’il Baghaei ya na fadar haka a yau litinin a taro da kafafen yada labarai da ya saba yi a ko wane mako. Ya kuma kara da cewa wanda aka nadan shi ne, Mohammad Reza Raouf Shaibani.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ya ce ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi ya dauki wannan matakin ne don fuskantar irin sauye-sauyen da ake samu a yankin a cikin yan kwanakin nan a kasar ta Siriya.
Ya ce, kasar Siriya tana da muhimmanci a yankin Asiya ta kudu don haka Iran ta na son ganin kasar Siriya ta dawo cikin hayyacinta bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad. Sannan mutanen kasar Siriya su sami cikekken yencin tafiyar da al-amuran kasarsu ba tare da shishigi daga kasashen waje ba.