Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Nasir Kan’ani ya bayyana muhimmancin girmama da kare tsaron manya da kananan ofisoshin jakadancin kasashe.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kara da cewa Da akwai damuwa a tattare da rahotannin da suke nuni da cewa a birnin Kito na kasar Ecuador an kutsa cikin ofishin jakadancin kasar Mexico.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ya kuma kara da cewa; Wajibi kowace kasa ta kare hurumin ofisoshin jakadancin da suke cikinta.
Shi da Glas ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar ne a karkashin shugaba Rafael Correa daga 2013 zuwa 2017.
Rikici a tsakanin kasashen biyu na yankin Latin ya yi kamari, ta yadda a ranar juma’ar da ta gabata, kasar Mexico ta yanke shawarar bai wa tsohon mataimakin shugaban kasa mai ra’ayin sauyi Glas mafakar siyasa.
A ranar juma’ar da ta gabata ne dai shugaban kasar Mexico Andress manuel Lopez Orbador ya rubuta a shafinsa na x cewa; An sanar da shi cewa, ‘yan sandan Ecudor sun bayar da umaranin a kutsa cikin ofishin jakadancin domin kama Glas, wanda yake neman mafaka saboda takura masa da ake yi.”
An nuna wani hoton bidiyo da yake nuna yadda ‘yan sanda suke kai da komowa a zagayen ofishin jakadancin na Mexico.
Mexico ta sanar da yanke alakar diplomasiyya da kasar Ecudor saboda abinda ya faru.