Tashar talbijin din Almayadeen ta bayar da labarin da yake cewa; Ministan harkokin wajen Iran Abas Arakci ya gana da masu shiga Tsakani na kasar Qatar a birnin Doha da marecen jiya Talata.
Majiyar tashar talbijin din ta kuma ce; Ministan harkokin wajen na Iran Dr. Abbas Arakci ya mika bayanan da ya karba daga masu shiga tsakanin na kasar Qatar ga shugaban kasa Mas’ud Pezeshkiyan a yayin taron majalisar ministoci a yau Laraba.
Majiyar ta kuma ce, sabanin da yake a tsakanin Amurka da Iran yana tattare ne a cikin batutuwan da ya kamata a fara bai wa muhimmanci wajen fara tattauna akansu.
Iran dai ta sha jaddada cewa akan yarjejeniyar Islamabad ne za a dora duk wata tattaunawa da Amurka akan kawo karshen yaki da kulla yarjejeniya.
Shawarar da Iran ta gabatar dai ita, ta kunshi dakatar da wuta na tsawon kwanaki 7 da zai kunshi bude mashigar Ruwan Hurmuz a rana ta 6 sannan a fara tattaunawa a rana ta 7.