Sakataren majalisar koli na tsaron kasar Iran Mosen Rezaei ya bayyana cewa akwai al-amura uku da suke daga cikin duk wani huldar zaman lafiya da Amurka a kasar Lebanon kadai. Saboda alamuran tsaro a kasar Lebanon yana da muhimmanci sosai a wajemmu.
Rezaei ya fadawa tashar talabijan ta Al-Manar na kungiyar Hizbullah haka, ya kuma kara da cewa, duk wani yaki a yankin zai iya shafar sauran wurare a yankin. Don haka ya bukaci a kawo karshen dukkan yake yake a yankin wadanda suka hada da kudancin Lebanon Gaza da sauran wurare. Sannan ya kara da cewa birnin Berut babban birnin kasar Lebanon musamman unguwar Dahiya ta kudancin birnon suna daga cikin jajayen layuka na kasar Iran.
Janar Rezaei ya ce kasashen yancin yammacin Asia suna nan kamar sarka ne, duk abinda ya taba daya daga cikinsu sai an ji kararsa a wata kasa a yankin, duk abinda ya rikita tsaro a yankin zai shafi bangarorin tattalin arziki siyasa da sauransu a kasashen yankin.
Sannan ya kammala da cewa kawo karshen yake-yake a kasashen yankin musamman na kasar Lebanon, janyewar sojojin HKI daga kudancin kasar Lebanon da kuma kawo karshen yaki a gaza na daga cikin al-amuran da zamu gabatar a cikin sharuddan ganawa da Amurkawa idan sun zabi dawowa kan teburin tattaunawa.
Daga karshe yace Iran tana bibiyan a kusa, duk abubuwan da suke faruwa a kasar Lebanon musamman kudancin kasar.