Jami’an gwamnatin Amurka sun bada labarin cewa zasu takaida hulda da wani bankin kasar Masar da ke AUE a tsarin bai daya na hada hadan kudade ta duniya a shirinta na takura tattalin arzikin kasar Iran.
Jaridar Arabnews ta kasar Saudia ta nakalto wata majiyar baitul malin Amurka na fadar haka a yau Jumma’a. Ya kumakara da cewa, Amurka zata yanke hulda da bankin ‘Banki Misr’ banki na biyu a girma mallakin gwamnatin kasar Masar daga tsarin SWIF na hada hadan kudade tsakanin bankuna a duniya na Amurka.
Labarin ya kara da cewa, wannan yana daga cikin matakin da sakatren baitul Malin Amurka ya fara dauka don tursasawa kasashen duniya daina hulda da Iran a fagen tattalin arziki. Kuma katsewar zata fara ne nan da kwanaki 30 bayan an ji maida martanin a kan lamarin daga wadanda suka dace a ji ra’ayinsu a Amurka.
Bayan watanni 6 da farwa kasar Iran da yaki wanda Amurka da HKI suka yi, Sakataren baitul Malin Amurka Scott Bessent ya kuduri anniyar gurgurta tattalin arzikin kasar Iran, wacce zata tilasta mata mika kai ga bukatun kasar. Ya kuma sha alwashin ladabtar da duk wata kasa wacce taki yin biyayya ga umurninta na katse huldar kasuwanci da tattalin arziki da Iran.
Ya zuwa yanzu dai masana suna ganin akwai matsaloli da dama wadanda Amurka zata fuskanta idan ta ce sai ta gama kowa da kowa a cikin shirinta na gurgunta tattalin arzikin kasar bIran. Saboda kasar China ne take huldae kasuwanci mafi girma da kasar Iran, don haka takura mata zai shafi hatta tattalin arzikin Amurka kanta.
Bessent ya fadawa ‘ Financial Times’ kan cewa zai halarci taron G20 a Asheville na jihar Carolaina a mako mai zuwa don magana da kasashen kan wannan batun. Kuma zai dorawa manajar Bank Millan na Iran a Dubai takunkumai, da wani kamfani a Singapore mai bawa kasar Iran kudade.