Amurka Ta Kara Yawan Yan Najerya Da Zata Tasa keyarsu Zuwa Gida

Ma’aikatar al-amuran tsaron cikin gida ta Amurka (DHS) ta kara sunayen yan Najeriya 10 daga cikin mutane 124 da ta bayyana sunayensu a cikin wayan

Ma’aikatar al-amuran tsaron cikin gida ta Amurka (DHS) ta kara sunayen yan Najeriya 10 daga cikin mutane 124 da ta bayyana sunayensu a cikin wayan Yunin da ya gabata, wadanda zata tasa kiyaesu zuwa gida.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto shafin yanar gizo na DHS yaba bayyana sunayen mutanen 10, yana kuma bayani kan cewa su masu aikata manya manyan laifuka ne, wadanda suka hada da zamba, safarar kwayoyi, mallakar makamai ba da izini ba da sauransu.

Kafin haka dai, hukumar ta DHS a ranar 09 ga watan Yuli 2026 ta bayyana sunayen yan Najeriya 124, wadanda jami’an shige da fice na kasar  wato ICE suka kama a jihohi da dama a kasar, don tasa keyarsu zuwa Najeriya, saboda ba’a bukatansu a kasar Amurka. Ko kuma suna zaune a kasar ba bisa ka’ida ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted