Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba ta aikawa kasar Rasha makamai don taimaka mata a yakin da take fafatawa da kasashen yamma a kasar Ukraine ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a shafinsa na X a safiyar yau Laraba ya kuma kara da cewa: A wannan karon ma gwamnatocin kasashen yamma sun yi kuskure a lissafinsu, dangane da amincewa da rahoton karya wanda kuma bisa kanta suka kakabawa kasarsabbin takunkuman tattalin arziki.
Ministan ya kra da cewa takunkuman tattalin arzikin da wasu kasashen Yamma suka dorawa kasar saboda labarin karya da suka samu ba zasu taba warware matsalolin da ke tsakaninsu da Iran ba, kuma zasu kara haddasa sabbin matsaloli ne a tsakaninsu.
Kafin haka dai kafafen yara labarai na kasashen yama musamman tashar talabijin ta CNN ta watsa wani rahoto wanda yake nuna cewa gwamnatin JMI ta aikewa kasar Rasha makamai masu linzami masu kuma cin karamin zango saboda tallafa mata a yakin da take fafatawa da kasashen yamma a Ukraine.