Shugaban hukumar ayyukan sararin samaniya na kasar Iran ya gabatar da matakai uku na cilla taurarin yan adam zuwa sararin samniya wadanda suke kaiwa tazarar kolimita 36,000 daga doron kasa, wadanda kuma za’a yi amfani da su a cikin al-amura da dama wadanda suka hada da sadarwa da kuma wasu al-amura.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Hassan Salareyeh yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa a halin yanzu tauraron dana dam mai suna Nahid -3 a shirye yake a cilla shi, sannan ana ci gaba da aiki kan wasu.
Salareyeh ya ce, a mataki na biyu akwai aikin gina kombo wanda zai kai tauraren sararin samani, a wasu sannanin wurare a kan falakin da ya dace, sannan daga baya suna da kayakin aiki wadanda zasu kara zuwa da su sama har zuwa tazarar kolimita 36,000 daga doron kasa inda zasu fara ayyukansu.
Yace, kombon da ake bukata sune masu daukan taurari masu nauyi, wadanda suka hada da Qaem 120 da kuma Phoenix (Qoqnoos ) wanda suke amfani da makamashi na ruwa ruwa da farko sannan bayan sun kai wani matsayi a sararin samani su fara amfani da wani makamashi na musamman don irin wancan yananin.