Iran Ta Fara Karban Sakonni Na Farko Daga Tauraron Dan’adama Mai sunan ‘Chamran 1” Wanda Ta Cilla A Safiyar Yau Asabar

Tauraron dan’adam mai suna “Chamran 1” wanda hukumar sararin samaniya na kasar Iran ta cilla zuwa sararin samania a safiyar yau Asabar ya isa inda

Tauraron dan’adam mai suna “Chamran 1” wanda hukumar sararin samaniya na kasar Iran ta cilla zuwa sararin samania a safiyar yau Asabar ya isa inda iake bukatar ya isa, kuma har ya fara aika sakonni daga sama zuwa kasa kamar yadda aka tsara.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa masana fasahar sararin samania a nan Iran sun yi amfani da kumbo mai suna “Qa’im100” wanda yake amfani da sandarerren makamashi don isar da tauraron ‘Chamran1’  zuwa nisan kilomita 550 daga kasa.

Labarin ya kara da cewa ‘Chamran1” yana da nauyin kilogram 60, sannan babban aikinsa shi ne gudanar da ayyukan bincike kan na’urorin da manhajojin kayakin lantarki daban daban a sararin samaniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments