Search
Close this search box.

Iran Ta Dorawa Wasu Jami’an Gwamnatin Amurka Takunkuman Tattalin Arziki Saboda Murkushe Amurkawa Masu Goyon Bayan Falasdinawa Da Take Yi

Gwamnatin JMI ta dorawa wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannu a tursasawa Amurkawa wadanda suke allawadai da HKI saboda kisan kiyashen da takewa

Gwamnatin JMI ta dorawa wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannu a tursasawa Amurkawa wadanda suke allawadai da HKI saboda kisan kiyashen da takewa Falasdinawa a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto wata majiya a ma’aikatar harkokin wajen kasar a nan Tehran tana fadar haka a safiyar yau Laraba, ta kuma kara da cewa ta dauki wannan matakin kan wadanan jami’an gwamnatin Amurka ne saboda rawar da suka taka wajen murkushe Amurkawa wadanda suke allawadai da  HKI a ta’asan da take aikatawa a Gaza.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran ta sanyawa wadannan jami’an gwamnatin Amurkan takunkumai ne bisa dokar maida martini kan Amurka, na take hakin bi’adama da kuma ayyukan ta’addancin da take yi a duniya.

Labarin ya kara da cewa sunayen jami’an gwamnatin Amurka wadanda takunkuman gwamnatin JMI ta shafa, sun hada da William Hitchens shugaba tsarin cikin gida na jihar Geoegia, Major Eddie Grier kwamandan aiwatar da ayyukan tsaro na kasa, Linda Stump-Kurnick babban jami’ar yansanda mata ta farko ko UF’S,  Pamela Smith babban jami’in yansanda na birnin washintong, Scott Dunning babban jami’in dansanda mai taimakawa shugaban yansanda na birnin Washington,  Jeffry Carrol mataimakin shugaba UTPD,  Shane Streepy shugaban yansanda na Cox Boston,  Michael Cox, shugaban yansanda na reshen jami’ar  Indiana, shugaban yansanda reshen jami’ar Arizona Michael Thompson, da kuma shugaban ofishin yan sanda CSU na yankin ‘Long Beach’ John Brockie.

Takunkuman dai sun hada da hada su visar shiga JMI, kwace dukkan kadarorin da kudaden da suka mallaka a kasar Iran ko kuma a duk JMI take da ikon yin haka a duniya. Daga karshen sanarwan ta bukaci duka hukumomin JMI da abin ya shafa su aiwatar da takunkumin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments