Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta JMI Muhammad Eslami ya musanta farfagandan wasu kafafen yana labarai dangane da shirin Nukliyar kasar. Inda suke yada labaran da suke cewa kasashen yamma ne suka tilastawa JMI amincewa da kara masu bincike a cikin shirinta na makamacin Nukliya.
Tashar talabijan ta Presstv ta nakalto shugaban hukumar makamshin Nukliya ta kasar Iran yana cewa, Iran ta amincewa karin masu sanya ido na hukumar IAEA su shigo kasar ne, don sanya ido a kan shirin nata ne, don ta fadada shirin da ta yi.
Yace: hukumar IAEA ta bukaci kara yawan masu sa ido a kan ayyukan nukliya na kasar Iran, ita kuma da amince da hakan.
Daga karshen Muhammad Eslami ya kammala da cewa HKI ce ta ke ingiza wasu gwamnonin hukumar ta IAEA, musamman wadanda suka fito daga kasashen yamma ko suke dasawa da su, don takurawa kasar Iran. Amma amincewar da ta yi da bukatar, don toshe duk wata daman da hukumar za ta kawo na cewa Iran bata bada hadin kan da ya dace. Banda haka bata da abin boyewa a cikin shirin nata.