Mukaddashin Ministan harkokin wajen Iran Ali Baqiri Kani a yayin juyayin tunawa da ranar da Amurka ta harbo wani jirgin saman fasinjan Iran da makami mai linzami a shekara ta 1988, wanda ake kira da “ranar fallasa manufar kare hakkin dan Adam na Amurka” a kalandar Iran, ya bayya na cewa: Tauye hakkin al’ummar Iran da Amurka ke yi a ko da yaushe yana bayyana ne ta hanyar da ba ta dace ba, ciki har da sanya musu takunkumai na rashin adalci.
Kani ya kara da cewa: Shekaru 36 da suka gabata ke nan da harin matsorata da ta’addanci da Amurka ta kai kan jirgin fasinja na Iran a sararin samaniyar Tekun Fasha.
A shafinsa na dandalin X, makaddashin ministan harkokin wajen Iran Baqiri Kani ya jaddada cewa: Gagarumin tallafi da Amurka take bai wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a muggan laifukan da take aikatawa kan Falasdinawa, hakan ya kara bayyana hakikaninta ga al’ummun duniya.
Ya kuma kara da bayyana wani sabon shafi a tarihin shugabannin Amurka da suka aikata laifukan kisan kiyashi, halaka jama’a, da kuma kakabawa jama’a takunkumai a bisa tubali na zalunci.