Iran Ta Bayyana Samuwar Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Gabas Ta Tsakiya A Matsayar Fitina

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Samuwar gwamnatin yahudawan sahayoniyya a yankin gabas ta tsakiya yana haifar da hargitsi a yankin Mukaddashin shugaban Jamhuriyar

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Samuwar gwamnatin yahudawan sahayoniyya a yankin gabas ta tsakiya yana haifar da hargitsi a yankin

Mukaddashin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Mokhber ya jaddada cewa: Hakikanin yahudawan sahayoniyya suna wakiltar kungiyar tsaro ta NATO ce, don haka kasancewar wadannan baki ‘yan kasashen waje a yankin yana haifar da rudani a yankin Kafqaz.

Mokhber ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev a jiya Laraba, da ya zo Iran don jajantawa gwamnati da al’ummar Iran dangane da shahadar Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa, yana mai bayyana wannan lamari da cewa: Babban rashi ne kuma ba ga Iran kadai ba, har ma ga dukkan kasashen musulmi da al’ummar musulmi.

Mokhber ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla a ganawar karshe tsakanin marigayin shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da takwaransa na kasar Azarbaijan Ilham Aliyev.

Har ila yau, Mukaddashin shugaban kasar ya yaba da irin matsayin da gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Azarbaijan suka nuna na hadin kai da nuna juyayi ga shahadar shugaban kasar Iran. Yana mai cewa: Al’ummar Iran da Azarbaijan suna da alaka da zumunta da kusanci da ba zasu taba rabuwa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments