Baqaei: Iran Tana Sanya Ido Kan Abin Da Ke Faruwa A Kudancin Caucasus

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kudancin Caucasus cikin lura Kakakin ma’aikatar harkokin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kudancin Caucasus cikin lura

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i, ya yi nuni da yadda Iran ke daukan abubuwan da ke faruwa a yankin arewa maso yammacin kasar da muhimmanci, yana mai jaddada cewa: “Suna sanya idanu kan abubuwan da suke faruwa, kuma ba sa sassauci ko daukarsa da rashin muhimmanci.”

A wata hira da aka yi da shi ta kafar yada labarai, Baqa’i ya fayyace matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan abubuwan da suke faruwa a yankin Kudancin Caucasus na baya-bayan nan, inda ya jaddada muhimmancin siyasa, tattalin arziki da siyasa a yankin ga Iran da kasashe makwabta musamman Rasha.

Ya kara da cewa: “Suna bin diddigin abubuwan da suka faru cikin lura,  ba sa sakaci a ko wane irin lamari, suna kuma jaddada wajibcin kaucewa yin tafsirin da ba daidai ba, ko yada bayanan da ba daidai ba, saboda wasu fassarori suna dogara ne kan bayanan da ba su dace ba, kuma suna iya yin illa ga dangantakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen kudancin Caucasus.”

Baqa’i ya kuma yi kira da a yi taka-tsan-tsan wajen amfani da kalmomin da kan iya haifar da rashin fahimta.

Dangane da batun soke tsawaita kan iyakar Armeniya, ya bayyana cewa: “Matsayinsu a fili yake, sun yi imanin cewa dole ne a bi wannan batu cikin taka-tsantsan da lura.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted