Iran: Shishigin Amurka A Cikin Al-Amuran Afganistan Yana Kara Rikita Al-Amura  A Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa ci gaba da shishigin da gwamnatin kasar Amurka take yi a cikin al-amuran kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa ci gaba da shishigin da gwamnatin kasar Amurka take yi a cikin al-amuran kasar Afganistan, yana kara rikita kasar.

Kamfanin dillancinn labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Abdullahiyan yana fadar haka a jiya Litinin a lokacinda yake ganawa da wakiliyar babban sakataren MDD a kasar Afganistan a nan Tehran.

Ya kuma kara da cewa JMI zata ci gaba da tallafawa shirin MDD a kasar Afganistan don kyautata al-amura a cikin kasar.

Ministan ya ce a halin yanzu kasar Iran tana daukar bakwancin miliyoyin mutanen kasar Afganistan,  kuma tana daukansu  a matsayin makobta, yan’uwa musulmi sannan wadanda suke da al-ada iri guda.

Roza Otunbayeva, wikiliyar Antonio Guterres a kasar Afganistan, a nata bangaren ta yabawa JMI kan irin gudumawar da take bayarwa don tabbatar da zaman lafiya a kasar Afgansitan.

Ta kuma gabatar da irin ayyukan da MDD take yi a kasar a halin yanzu,  da kuma sauye sauyen da ke faruwa a kasar. Otunbayeva, ta ce MDD tana shirin fara taron Afganistan karo na 3 ko ‘dauha na 3’ wanda za’a gudanar, nan gaba a birnin Doha na kasar Qatar.

Ta Kuma bukaci halattar kasashen da suke makobtaka da kasar Afganistan daga ciki har da JMI . Kuma  za’a tattauna abubuwan da suka shafi kasar ta Afganistan daga ciki har da matsalolin tsaro a kasar.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments