Sakatarin majalisar koli na tsaron kasar Iran Mohsen Rizaei ya bayyana cewa, idan makiya sun sake farwa JMI to kuwa, zasu fuskanci maida martani mai tsanani kuma mai rushewa, tare da amfani da sabbin makamai wadanda basu taba sanin irinsu ba.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Rezaei yana cewa, har zuwa lokacinda zasu taba wannan kuskuren, Iran a shirye take ta dawo kan hanyar diblomasia, idan sun aiwatar da sharuddan kasar guda 7.
Yace, ‘mun sha nanata cewa, aiwatar da sharuddan kasar guda 7, su ne kawai zasu sa JMI ta dawo kan teburin tattaunawa da makiya. Don haka kada su bari sai an rufe kofar.
Yace, idan sun kuskura suka dauki matakin soje a kan kasar Iran, zamu aiwatar da umurnin Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar na maida martani mai tsanani kansu.
Kafin haka dai Aya. Mojtaba Hussaini Khaminaei, ya gana da manya manyan kwamandojin sojojin JMI inda ya bukaci su yi shirin maida martani mafi tsanani kan makiya, tare da amfani da sabbin kayakin yaki na zamani don samun garkuwa daga makamansu da kuma maida martani mai tsanani.