Search
Close this search box.

Iran: Martaninmu Kan isra’ila Ba Shi Da Wata Alaka Da Batun Tsagaita Wuta A gaza

Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na daukar fansa kan ta’addancin Isra’ila a cikin Iran ba

Wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na daukar fansa kan ta’addancin Isra’ila a cikin Iran ba shi da alaka da tattaunawar tsagaita bude wuta da ake yi kan zirin Gaza.

Wakilin na Iran ya ce, tsagaita bude wuta mai ɗorewa a Gaza shine fifiko a gare mu, duk wata yarjejeniya da Hamas ta amince da ita za mu amince da ita, amma kuma wanann ba shi da alaka da hakkin da Iran take da shin a mayar da martani kan Isra’ila, dangane da shishigin da ta yi a cikin kasar wajen kisan Isma’il Haniyya.

Tawagar ta ce “An keta hakkin tsaron kasarmu da ‘yancinmu a lokacin ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a baya-bayan nan. Muna da ‘yancin kare kanmu ta hanyar mayar da martani kan hakan.

Ofishin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kuma yi magana game da hanyoyin sadarwa tsakanin Iran da Amurka.

“A koyaushe akwai tashoshi kai tsaye na hukuma don isar da sakonni tsakanin Iran da Amurka,” in ji tawagar.

 (IRGC) sun bayyana cewa Haniyeh ya yi shahada ne sakamakon wani makami mai linzami da aka harba daga wajen masaukinsa a birnin Tehran.

Jagorori na siyasa da na soja na Iran da suka hada da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei da kuma shugaban kasar Masoud Pezeshkian sun sha alwashin daukar fansa kan jinin Haniyyah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments