Iran : Kuna Bangaren Tarihi Na Gaskiya” Wasikar Jagora Ga Daliban Jami’o’in Amurka

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid aliyul Khaminae ya fadawa daliban jami’o’in Amurka wadanda suke goyon bayan al-ummar Falasdinu a yakin da gwamnatin

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid aliyul Khaminae ya fadawa daliban jami’o’in Amurka wadanda suke goyon bayan al-ummar Falasdinu a yakin da gwamnatin kasarsu take da hannu dmudmu a cikinsa, kan cewa suna bisa bangaren da yake da gaskiya a tarihi.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto jagoran yana fadara haka a wata wakisa da musamman day a rubutawa daliban a yau ALhamis.

Wasikar ta cewa gaba da cewa, kuna cikin wadanda suke gwagwarmaya don taimakawa wadanda aka zalunta kuna kuma turjiya ga azzaluman shuwagabannin kasar Amurka  wadanda suke bawa HKI duk tallafin da take bukata a yakin da take fafatawa a Gaza. Daga karshen jagoran ya bayyana cewa yana tare da su a matsayin da suka dauka.

Tun cikin watan Afrilun da ya gabata ne dubban daliban jami’o’i a kasar Amurka da wasu kasashen yamma suka fara zaman dirshen a cikin harabobin jami’o’insu don tursasawa gwamnatocin  kasashensu su dakatar da tallafin da take bawa HKI, sannan su kawo karshen yaki a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments