Search
Close this search box.

Iran: Kudurin IAEA ba zai iya yin illa ga ci gaban shirin nukiliyarmu ba

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan matakin da hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta dauka, kan wani kuduri

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan matakin da hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta dauka, kan wani kuduri na adawa da Iran, tare da jaddada cewa irin wannan matakin ba zai kawo cikas ga shirin nukiliyar kasar na ayyukan zaman lafiya ba.

Ma’aikatar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Larabar da ta gabata bayan da kwamitin gudanarwar hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya zartas da kudurin, inda ya zargi Jamhuriyar Musulunci ta Iran da yin watsi da hadin gwiwa da hukumar.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, “Shafin kudurin ba zai yi wani tasiri ba kan kudurin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da amfani da makamashin nukiliya domin ayyukan farar hula, da kuma aiwatar da shirye-shiryenta na raya kasa, bisa la’akari da hakkokin da aka bai wa kasar bisa yarjejeniyar kasa da kasa.”

Bayanin y ace, hukumar IAEA Ta dauki kudurin a matsayin “manufar siyasa da ba ta da amfani” da kuma yunkurin wasu kasashen yammacin duniya na yin amfani da damar siyasa ta hanyoyin cibiyoyin  kasa da kasa don cimma wadannan manufofi nasu.

Iran ta sha nanata cewa tana gudanar da shirye-shiryen samar da makamashin nukiliya ne domin ayyukan farar hula da ci gaban kasa, bis asanya ido na jami’an hukumar ta IAEA.

Har ila yau, kasar ta sha bayyana shirye-shiryenta na warware sabanin da ke tsakaninta da hukumar ta IAEA bisa tsarin hulda mai inganci da hadin gwiwa da fasaha.

Sanarwar ma’aikatar ta kuma bayyana cewa “Iran ta kuduri aniyar ci gaba da hadin gwiwa tare da hukumar a cikin tsarin haƙƙinta na ƙasa da ƙasa dangane da yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) da yarjejeniyar kariya ta hukumar.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments