Iran: Kasashen Turai 3 Ne Da Alhakin Duk Matakan Da Iran Zata Dauka Dangane Da Kuduri Mai Sukan Shirin Nukliyar Kasar A Hukumar IAEA

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da suke Vienna ya bayyana cewa kasahen uku, wato Faransa, Butania da kuma Jamus ne da alhakin duk wani

Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD da suke Vienna ya bayyana cewa kasahen uku, wato Faransa, Butania da kuma Jamus ne da alhakin duk wani mataki ko matakan da JMI zata dauka kan kudurin da gwamnonin hukumar IAEA suka fitar kan shirin Nukliyar kasar Iran.

Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Mehsen Naziri Asl yana fadar haka  bayan da gwamnonin hukumar ta IAEA suka bayyana rashin amincewarsu da irin hadin kan da JMI take bawa hukumar ta IAEA a cikin shirinta na makamashin nukliya.

Naziri Asl ya kara da cewa wannan kudurin babu shakka zai bata dangantaka mai kyau da ke tsakanin JMI da kuma hukumar IAEA. Sannan ya kara da cewa JMi daga yanzu kuma ba zata saurari hukumar ta IAEA a cikin duk wata bukata wacce bata zama lazini kan Iran bisa sansanin dokokin hukumar ba.

Daga karshe ya bayyana cewa wadannan kasashen uku wanda suka jagoranci sauran gwamnonin hukumar a sukan da suka yiwa JMI su zasu kuka da kansu kan duk matakan da JMI ta dauka nan gaba.

Ya kuma kara da cewa wadannan kasashe suna sun kare HKI ne kan ta’asan da take aikatawa a kasar Falasdinu da ta mamaye, su maida hankalin duniya kan kasar Iran.

Gwamnoni 20 ne suka tabbatar da rahotanni kan shirin nukliyar kasar Iran wadanda wadannan kasashe uku suka gabatar, a yayinda kasashe 2 suka ki amincewa da su, sai kuma kasashe 12 suka ki kada kuri’unsu.

Kudurin dai ya bayyana cewa JMI bata bada cikekken hadin kai ga hukumar IAEA don aiwatar da ayyukanta a cibiyoyin Nukliya na kasar, kuma ya bukaci hukumar ya ci gaba da neman hadin daga kasar Iran don gudanar da ayyukanta.

Sai dai hukumar makamashin nukkliya ta kasar Iran ta bayyana cewa wannan kudurin ba zai yi tasiri a cikin ayyukan da ta sa a gaba a cibiyoyinta na makamashin nukliya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments