Iran: Kasar Siriya Tana Fuskantar Jarrabawa Mai Tsanani Daga ‘Yan Ta’adda, Amurka Da Mamayar Kuma HKI

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kasar Siriya tana fama da jarrabawa mai tsanani daga hannun yanta’adda da mamayar Amurka da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kasar Siriya tana fama da jarrabawa mai tsanani daga hannun yanta’adda da mamayar Amurka da HKI.

Jaridar Al-Akhbar ta gasar Lebanon ta nakalto ministan ya na fadar haka a yau Asabar. Ya kuma kara da cewa mamayar da gwamnatocin Amurka da HKI suke yi kasar Siriya da kuma tsoron bayyana yan ta’adda ta Kungiyar Daesh da kuma Al-qaeda a kasar ta siriya jarrabawa ce babban ga kasar.

Ministan ya ce manufar wadannan kasashe shi ne wargaza tsarin zamantakewa a kasar Siriya, bayan haka suna son ganin kasar Siriya, ba zata iya tabuka kome a wajen kare kanta daga hare-hare HKI da kuma Amurka nan gaba ba.

Daga karshe ministan ya bayyana cewa akwai fatan mutanen kasar za su farka, su kuma yi abinda ya dace don kawo karshen mamayar da sojojin Amurka da kuma HKI suke yi wa kasar, tare da taimakon wasu kasashen yankin.

Yace abinda yake faruwa a Gaza, wani babban masali ne ga mutanen Siriya na turjiya ga yan mamaya.

Kuma ko menene dadewar mamayar, sai mutanen kasar sun dawo kan gwagwarmaya da yan ammayar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments