Iran : Jagora ya ziyarci kabarin Imam Khomeini gabanin bikin cika shekaru 47 da juyin Musulunci

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ziyarci kabarin marigayi Imam Khomeini, wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci, a jajibirin cika

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ziyarci kabarin marigayi Imam Khomeini, wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci, a jajibirin cika shekaru 47 da juyin juya halin Musulunci.

A yayin ziyarar, Ayatollah Khamenei ya yi addu’o’i a wurin tare da sake amincewa da manufofin Imam Khomeini.

Jagoran ya kuma girmama shahidan juyin juya halin Musulunci.

Ziyarar Jagoran ta zo ne duk da wasu rahotanni, ciki har da na gidan talabijin na ‘Iran International’, wanda ke zargin cewa Ayatollah Khamenei yana “ɓoye a cikin wani matsuguni na karkashin kasa” a Tehran a lokacin da ake kara samun rikici tsakaninsa da Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari kan Iran bayan ya tayar da rikici a farkon wannan watan ta hanyar kiran masu zanga-zanga dauke da makamai dasu kwace cibiyoyin gwamnati tare da yi musu alkawarin cewa “taimako yana kan hanya.”

Rikicin ya haifar da barna mai yawa ga kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted