Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalen mamatan ifti’la’in fashewar data auku a mahakar ma’adanai ta a garin Tabas da ke gabashin kasar.
Jagoran a cikin sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan ya jaddada; bukatar tura duk abinda akebukata na samar da agaji ga ma’aikatan da abin ya shafa ko kuma suka makale a cikin mahakar.
Gwamman mutane ne suka rasa rayukansu a lamarin da ya faru da misalin a daren Asabar.
Tunda farko kafofin yada labaren kasar sun ce akalla mutum 31 ne suka rasa rayukansu kuma wasu da dama sun jikkata a lamarin.
An ruwaito cewa fashewar sinadarin methane ce ta afku a wasu sassa biyu na wurin hakar ma’adinan a garin Tabas mai tazarar kilomita 540 a kudu maso gabashin Tehran, babban birnin kasar.