Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ya jaddada cewa, Isra’ila ba za ta iya shiga wani sabon yaki da kasar Labanon ba, yayin da take kokarin janyewa daga tarkon da ta jekfa kanta a yankin zirin Gaza.
Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai a ofishin jakadancin Iran dake birnin Beirut na kasar Labanon, inda ya ce, babban tsarin siyasar harkokin wajen kasar Iran cibiyoyi ne na kasar.
Ya kuma jaddada cewa wadannan manufofi sun samo asali ne daga tsarin shugabanci da tafiyarwa ta Jamhuriyar Musulunci, wanda ba za su rushe ba saboda rashin wasu jami’ai masu tafiyar da su.
Bagheri Kani ya zabi kasar Labanon ne a ziyararsa ta farko a kasashen waje, inda ya ba da misali da rawar da al’ummar kasar ke takawa a matsayin gishiki na gwagwarmaya, bugu da kari kan hakan kuma da alaka mai karfi tsakanin al’ummar Iran da na Lebanon. Ya bayyana godiyarsa ga gwamnati da al’ummar kasar Labanon bisa hadin kan da suka ba, Iran biyo bayan hatsarin da ya yi sanadin rasuwar shugaba Ibrahim Raisi da mukarrabansa.
Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya nanata irin goyon bayan da Iran ke baiwa dakarun soji, da jama’a da kuma ‘yan gwagwarmaya kasar Lebanon ba tare da yin kasa a gwiwa ba, yana mai bayyana alakar da ke tsakanin kasashen biyu a matsayin “tabbatacciyar alaka.” Ya sake jaddada kudirin Iran na samar da man fetur da dangoginsa ga kasar Labanon, da kuma cikakken goyon bayan da Tehran ke baiwa birnin Beirut domin kare kanta daga shishigi na Isra’ila.
Sanann kuma ya yi tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a Gaza, inda ya bayyana cewa gwagwarmayar Palasdinawa na da cikakkiyar damar yanke shawara kan makomarta, da kuma dauukar matakan ad suka dace. Ya kara da cewa shekaru 75 al’ummar Palastinu suna gwagwarmayar kare mutuncinsu da kasarsu da kuma makomarsu.
Bagheri Kani ya ce, “Bayan watanni takwas na yaki a Gaza, mun ga cewa Washington, babbar mai goyon bayan yahudawan sahyuniya ‘yan mamaya, tana ba da shawarar kawo karshen yakin.”