Iran: Israila Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Ga Lebanon

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da hare haren da haramtacciyar kasar Israila ta ke ci gaba da kaiwa kudancin kasar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da hare haren da haramtacciyar kasar Israila ta ke ci gaba da kaiwa kudancin kasar Lebanon, ya kuma kara da cewa, hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa kuma suna barazana da yarjeniyar zaman lafiyan da aka cimma a cikin watan Nuwamban shekara ta 2024.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a yau Lraba, ya kuma kara da cewa wadan nan hare hare sune suke hana kasar Lebanon samun cikekken yanci. A yau ne kasar Lebanon tane tunawa da zagayowar ranar samun yencin kan kasar.

Ministan ya kara da cewa babbar barazana ga yencin kai da zaman lafiya da kuma mutuncin kasar Lebanon itace isra’ila.

Ministan yace nauyi ne kan kwamitin tsaro na MDD ta tabbatar da cewa, Isra’ila ta kawo karshen mamayar da takewa kudancin kasar Lebanon, amma bata yi hakan ba. Banda haka gwamnatin kasar Amurka ta bayyana rashin adalci a goyon bayan HKI kan manufofinta a kasar Lebanon da yankin.

Ya kuma kara da cewa, kwamitin tsaro ne yakamata ya tashi ya kawo karshen mamayar da Isra’ila takewa kudancin kasar Lebanon da yankunan kasar Siriya da Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan.

Daga karshe ministan ya ce: shirin Amurka na abinda ta kira zaman lafiya a kasar Lebanon shiri ne wanda mutanen kasar basu amince da hakan ba, kuma ba zai taba amfaninsu ba.

Daga karshe Aragchi ya yabawa kungiyar Hizbullah wacce ta tsaya tsayin daka don kare kasar da mamayar Isra’ila. Y ace Iran tana tare da ita kuma zata ci gaba da taimaka mata don kiyaye mutuncin kasar da samun cikekken diyauci daga makiyanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted