Iran: Inda Makiya Kasar Sun San Cewa Zasu Sami Nasara A Kan Iran A Yaki Da Tuni Sunn Farmata Da Yaki

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa da Amurka da HKI sun san cewa zasu sami nasara a kan kasar Iran da

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa da Amurka da HKI sun san cewa zasu sami nasara a kan kasar Iran da yaki da tuni  sun fadawa kasar sun kuma mamayeta.

Amma saboda wannan tsoron ne suka zabi tattaunawa da ita a kan shirinta na makamshin nukliya. Sannan Shirin makamacin nikliya ma daya ne kacal daga matsalolin da ke tsakanin Iran da HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka.  Ya ce akwai matsaloli da dama, tana jirin ta kamala da gudu don ta bullo da wata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya da yamma ya kuma  kara da cewa, manufar Iran ta shiga tattaunawa da Amurka ita ce, samun ganin an daukewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. Kuma ta zabi  hanyar diblomasiyya don samun hakan.

Arachi ya bayyana cewa kasashen yamma musamman Amurka sun dorawa kasar takunkuman tattalin arziki masu yawa, amma mafi  muhimmanci daga cikinsu su ne na makamashin nukliya, don Shirin makamashin nukliyar kasar ne Amurka ta dora mata takunkuman hana saida man fetur ta kuma rana bankunan kasar Iran da Swift, wato aikin da sauran bankunan a duniya. Kuma su ne suka fi cutar da tattalin arzikin kasar.  Daga karshe Aragchi ya bayyana cewa in akwai hanyar cira wadannan takunkuman Iran ba zata yi jiunkiri ba, amma kuma tana rayuwa da takunkuman tun shekar ta 2018. Amurka ta kasa cimma manufarta don wadannan takunkuman wanda kuma shine takurawa mutane su tashi su kifar da gwamnatin JMI wanda bai faru ba kuma ba zai faruba.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted