Shugaban hukumar Makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasarsa na kalubalantar na kasashen yamma saboda su suna son kebe wannan ilmin da kuma fasahar ga kansu ne kadai, wanda zai ci gaba da basu damar danni sauran kasashen duniya. Wannan, a yayinda ilmin da fasahar a wajen Iran nu duk wanda yake iya amfani ko ya sarrafa shi ne.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaba hukumar (AEOI) yana fadar haka a jiya Talata, 14 ga watan Octoba, a kuma taron kasa ta ‘Ranar samarda kayaki masu inganci ta klasa’ wato ‘National Standard day’.
Ya ce gaskiyar al-amarin shi ne, kasashen yamma suna adawa da ilmi da kuma fasahar Nukliya ta kasar Iran, sai dai wannan adawar ta su ba zata canza kome a kan shirin nukliyar kasar ba.
Eslamu ya ce kasashen yamma ba zasu taba barin adawa da shirin nukliyar kasar Iran ba, saboda idan sun daina adawa da shirin ta babu kuma wani abu da zasu kama don ci gaba da sukarta.
Yace fasahar Nukliya ta rika ta shiga cikin dukkan sassan kamfanonin wadanda suka hada da manya manyan kamfanoni kamar matatun man fetur, kamfanonin sinadaran man fetur wato Petro chemicals, da kuma kamfanonin samar da karafa.
Yace kasashen yamma musamman Amurka da HKI a cikin yake yaken da suka dorawa JMI sun yi kokarin latata wadan nan kamfanoni a kasar Iran saboda dakatar da ci gaban da kasar take samu.
An Ga Hayaki Na Tashi A Wani Ginin Kamfanin Aramco Bayan Gargadin Yemen
Ma’aikatar makamashi ta kasar Saudia ta bada sanarwan tashin wata a babban ginin kamfanin Aramco da ke birnin Riyad, kuma hakan ya faru ne jim kadan bayan gwamnatin kasar Yemen ta yi gargadi zata yi hakan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ma’aikatar na cewa an kai hari kan babban ginin harkokin gudanarwa na kamfanin Aramco wanda ya sa ya gama da wuta kuma ana iya ganin hayaki na tashi daga ginin.
Labarin ya kara da cewa a safiyar yau Laraba ma sojojin kasar Yemen sun cilla makamai kan ginin Aramco da ke Dahahran.
Gwamnatin ta ce ta kakkabo wasu daga cikin makaman da mayakan yemen suke ci gaba da cillawa kan kasar a yayinda ake fafatawa da sojojin kasar a cikin gudancin kasar ta Yemen wanda saudin take mamaye da shi tun shekara ta 2015.
Wasu kafafen yada labaran kasar sun bada labarin kakkabo wasu daga cikin makamai masu linzamu samfurin crusse daga kasar Yemen. Gwamnatin kasar Saudia a shekara ta 2015 ta mamaye gudancin Yemen da nufin bawa Tsohon shugaban kasar Aabdu rabbu mansur hadi damar komawa san’a a kan kujerar shugabancin kasar sannan ta dorawa gwamnatin san’a takunkuman tattalin arziki ta sama kasa da kuma ruwa, wanda a yau ya kai kimani shekaru 12. gwamnatin kasar Yemen tana bukatar dauke wadan nan takunkuman. CNN tace saudiya bata da zabi an banda tattaunawa da Yemen.