Iran ta yi gargadin cewa sabon harin da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen zai kara haifar da “rashin tsaro da rashin zaman lafiya” a yankin yammacin Asiya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da sojojin kawancen suka kai kan ababen more rayuwa a garin Sa’ada da ke arewa maso yammacin kasar Yamen, kwanaki kadan bayan da suka yi ruwan bama-bamai ta sama a lardin Hudaidah da ke gabar tekun yammacin kasar.
Baghaei ya ce ci gaba da kai hare-haren soji da Amurka da Birtaniya da gwamnatin Isra’ila ke yi kan kasar Yaman ya zama cin zarafi a fili kan ‘yancin kan kasar ta Yemen.
Ya kara da cewa hare-haren sun sabawa ka’idoji da dokokin kasa da kasa da kuma tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Kamfanin dillancin labaran Saba na kasar Yemen, ya nakalto majiyar kasar da ta nemi a sakaya sunanta, ta rawaito cewa, dakarun kawancen sojojin kasashen Yamma sun kai hare-hare ta sama guda uku a gabashin birnin Sa’ada babban birnin lardin a safiyar yau Lahadi.