Rundinar sojin Iran ta alakanta shan kayan da jam’iyyar Republican suka yi a zaben tsakiyar wa’adi na Amurka da gazawar sojojin kasar a yaki da Iran.
Kakakin Rundunar Sojin Iran ya bayyana cewa, duk wani karfi da ya yi yunkurin kalubalantar karfin Iran, da yardar Allah a karshe zai fuskanci wargajewa a idon duniya.
Birgediya Janar Abolfazl Shekarchi ya kawo misalai da suka hada da matsalolin da Amurka ta fuskanta, ciki har da koma-baya da Shugaban kasar Donald Trump da abokan siyasarsa na jam’iyyar Republican ke fuskanta a fannoni daban-daban.
Kakakin ya bayyana cewa, Trump da abokan tafiyarsa—wadanda ya siffanta da cewa “ba su da hikima, kuma ‘yan ta’adda”—sun kaddamar da hare-hare kan Iran da nufin ruguza wannan kasa.
“Sai dai, lamarin ya juya, inda su kansu suka zama wadanda suka shiga cikin matsalolin siyasa, rikice-rikicen cikin gida, da kuma shan kashi a hannun jaruman sojojin Iran da kuma kungiyoyin gwagwarmaya.”
Ya kuma yi magana kan mummunar shan kashin da jam’iyyar Republican ta yi a zaben tsakiyar wa’adi, wanda ya biyo bayan gazawar sojin Amurka a yayin da Iran ta mayar da martani.
Ya ce wannan shan kashi “ba wai kawai sakamakon sauye-sauye na wucin-gadi ba ne a siyasar cikin gidan Amurka,” hakan yana nuni ne ga “wani al’amari mai girma da ba za a iya musantawa ba: wato shan kashi a gaban Iran.”
Ya ce manufofin Washington na cin zarafi, kisa, da matsin lamba mai tsanani—da dabarun soji duk ba su yi tasiri ba, sun gaza a gaban karfin Iran da kuma kudirin shugabannin Jamhuriyar Musulunci, al’ummar Iran, da sojojinta.