Iran : Duk wata hanyar tallafawa Amurka wajen kai mana hari zata fuskanci martani

Hedikwatar tsaron Iran ta yi ikirarin cewa duk wata hanyar tallafawa “dakarun Amurka da ke kai hari” zata fuskanci martini. Wannan sanarwar ta biyo bayan

Hedikwatar tsaron Iran ta yi ikirarin cewa duk wata hanyar tallafawa “dakarun Amurka da ke kai hari” zata fuskanci martini.

Wannan sanarwar ta biyo bayan hare-haren sama na Amurka wanda Iran ta ce ya keta yarjejeniyar tsagaita wuta a fili kuma ya karya yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.

Hedikwatar ta bayyana a cikin sanarwar ta cewa duk wata kasa da sojojin Amurka ke amfani da yankinta ko kayan aikinta don kai hare-hare kan Iran za zata fuskanci martani daga sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Haka zalika Hedikwatar ta kuma sake nanata cewa hanya daya tilo da jiragen ruwa na kasuwanci da jiragen ruwa masu daukar mai za su bi ta Mashigin Hormuz ita ce wadda Iran ta ayyana, kuma Tehran ba za ta amince da wani shishigi a cikin harkokin gudanar da mashigin ba.

Waɗannan sabbin hare-haren sun faru ne yayin da Iran ke bikin jana’izar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, a Iraki.

Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta bayyana cewa hare-haren Amurka wani “yunkuri ne na neman dishe tasirin jerin tarurukan jana’izar da aka yi a Iran da Iraki ga Jagoran, wanda ya tsone idon makiya da kuma koma baya a siyasance ga Washington.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted