Iran: Duk Wani Gigin “Yan Sahayoniya Na  Kai Wa Kasar Hari Zai Fuskanci Martani Mai Tsanani

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Duk wani sabon hari da ‘yan sahayoniya za su kawo kan Iran, zai fuskanci

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Duk wani sabon hari da ‘yan sahayoniya za su kawo kan Iran, zai fuskanci mayar da martani mai tsananin gaske fiye da wanda su ka  gani a baya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin anan birnin Tehran ya bayyana cewa; Iran tana sa ido da bin diddigin duk wani motsi da karakainar ‘yan sahayoniya, kuma tana cikin jan damara a kodayaushe.

Dr. Baka’i ya kuma ce,Dabi’ar ‘yan sahayoniya ita ce samar da rashin tsaro a cikin wannan yankin da kuma wuce gona da iri,don haka dukkanin kasashen wannan yankin sun fahimci cewa, tsarin ‘yan sahayoniya babbar barazana ce ta tsaro da zaman lafiya ga duniya.”

Haka nan kuma ya ce, a fili yake cewa daga lokaci zuwa lokaci ‘yan sahayoniyar suna kai wa kasashe hare-hare, da hakan yake nuni da wannan halayyar tasu da kuma jefa yankin cikin rikici da tashin hankali.

Da yake Magana akan yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta dauki yankin Somaliland a matsayin kasa mai ‘yanci, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; Wannan furucin  ba shi da wata ma’ana ko kadan.”

Bugu da kari Dr. Baka’i ya kuma ce; Abinda kasar da ba ta da halarci take yi, shi ne kokarin tsittsinka kasashen musulmi, kuma tuni kungiyoyin tarayyar Afirka da na kasashen musulmi su ka yi tir da wannan matakin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted