Rahotanni sun bayyana cewa jami’an iran da wasu wakilan kasashe 12 sun fice daga dakin taron koli na cica da ake yi a birnin Baku lokacin da shugaban Isra’ila zai fara bayani a wajen, inda iran ta yi kira da ayi waje da wakilin isra’ila daga wajen taron baki daya.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran Kazem Ghariabadi yayi kira ga mambobin taron da su kori jamian gwamnatin isra’ila daga taron da ake gudanarwa na intarnational ana confidence building measure na yankin Asiya
wakilan da suka fice daga dakin taron sun hada da na kasashen palasdinu, Pakistan, Saudi arebiya, turkiya, Iraqi, masar, Kuwait, Qatar, Jordan, Malesiya, Indenosiya, da kuma kasar Bangaladash inda wakilan kasashen guda 13 suna wakiltar kusan rabin mahalarta taron da ya kunshi kasashe 28
Da yake jawabi a wajen taron mataimakin ministan wajen kasar iran Kazem Garibabadi ya bayyana isra’ila a matsayin tushen haifar da rashin tsaro da zaman lafiya a yankin asiya, kuma yayi kira ga kasashen dake mambobin taron da kada su yi gum da bakinsu kan mummunan laifukan yaki da gwamnatin isra’ila take tafkawa