Gwamnatocin kasashen Iran da Rasha sun kammala tsarin musayar kudade ta na’urori lantarki tsakanin kasashen biyu wanda ake kira ‘ Mir da Shetab’ , kuma a halin yanzu wannan tsarin da kuma shirin ya fara aiki a tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto gwamnan babban bankin Iran Muhammad Riza Farzi yana fadar haka a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa tsarin ‘Mir da Shetab’ ya bawa yan kasuwa daga kasashen Iran da Rasha damar daukar kudade daga na’urorin ATM na kasashen biyu dake kasashen su.
Gwamnan ya kara da cewa, fara aiki da wannan shirin ko tsarin dai, mataki ne na farko don bunkasa tattalin arzikin kasashen Iran ta Rasha, ba tare da shigar Dalar Amurka tsakani ba. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu wadanda suke da katin cire kudade na Shetab daga Iran suna iya daukar kudade ko kuma suyi sayayya a kasar Rasha da shi.
Hakama mutanen Rasha wadanda suka zo Iran suna iya saya ku daukar kudadensu a kasar Iran tare da amfani da katin banki na Mir dake hannunsu.
Kasashen biyu wadanda duk suke fama da matsalolin tattalin arziki saboda mamaye kasuwannin duniya da dalar Amurka tayi, a halin yanzu zasu gudanar da harkokin kasuwanci a tsakaninsu ba tare da shigar dalar Amurka a tsakanini ba.
A shekara 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta sa aka hana kasar Iran amfani da tsarin musayar kudade tsakanin bankuna a duniya da kuma kasuwancin da ake kira swift.