Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI da kuma kasar Japan suna iya jagorantar kasashen duniya zuwa ga rabata daga makaman kare dangi.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Ministan yana fadar haka a wani rubutu da yayi, wanda kuma aka buga a jaridar Asahi Shimbun ta kasar Japan. Ya kuma kara da cewa, kasashen biyu an yi amfani da makaman kare dangi a kansu. Y ace kamar yadda Amurka ta yi amfani da makaman nukliya kan kasar Japan a shekara ta 1945 a karshen yakin duniya na biyu, haka nan Sadam ya yi amfanin da makaman guba a kan iraniyawa a kallafeffen yakin da suka fafata na shekaru 8 a tsakaninsu.
Arachi ya ce, kasashen biyu a matsayin kasashen da aka yi amfani da makaman kare dangi a kansu suna iya samar da wata motsi a duniya wacce za’a iya kaiwa ga lalata dubban makaman kare dangi a duniya.
Ministan yayi wannan rubutun ne don taya kasar Japan jejen kashe dubban mutanen kasar da makaman nukliya a shekara 1945, wanda a yau yake cika shekaru 80 da faruwa.