Kamfanin gina tashoshin jiragen ruwa mai suna ‘Majdudu’ na kasar Indiya ya sanya hannu tare da gwamnatin kasar Iran don fara gina tashar jiragen ruwa ta ‘Shahid Behesti’ a garin Chabahar dake kudancin kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa Ministan hanyoyi da kula da birani na kasar Iran da kuma ministan tashoshin jiragen ruwa na kasar Indiya na daga cikin bakin da suka halarci bikin rattaba hannu kan wannan yarjeniyar a jiya litinin.
Labarin ya kara da cewa wannan aiki shi ne aiki mafi muhimmanci wanda kasashen biyu suka taba kullawa a tsakaninsu, kuma idan an kammala wannan aikin, kasashe da dama a yankin suna iya amfana da tashar jiragen ruwan, daga ciki har da kasar Afgansitan wacce kayakin da ke shigowa ko fitowa daga kasar suna iya yada zango a tashar kafin su wuce duk inda zasu je a duniya.