Iran Da Bahrain Na Tattauna Hanyoyin Maida Da Huldar Diflomatisyya A Tsakaninsu

Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Masarautar Bahrain sun amince da fara tattaunawa kan maido da huldar diflomatsiyya a tsakanin kasashen biyu bayan shafe sama da

Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Masarautar Bahrain sun amince da fara tattaunawa kan maido da huldar diflomatsiyya a tsakanin kasashen biyu bayan shafe sama da shekaru takwas da suka gabata.

Bangarorin sun bayyana hakan ne a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.

Sanarwar ta ce, an cimma yarjejeniyar ne bayan wata ganawa da ministan harkokin wajen Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani da takwaransa na Bahrain Abdullatif bin Rashid Al Zayani suka yi.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, manyan jami’an diflomasiyyar kasashen biyu sun gana bisa tsarin dangantakar ‘yan uwantaka da tarihi tsakanin Masarautar Bahrain da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da kuma alaka ta addini da makwabtaka.

Sanarwar ta kammala cewa, “A yayin ganawar, bangarorin biyu sun amince da samar da hanyoyin da suka dace don fara shawarwari tsakanin kasashen biyu kan yadda za a sake farfado da dangantakar siyasa” tsakanin Tehran da Manama.

Sanarwar ta zo ne bayan a farkon watan Yuni, Mohammad Jamshidi, mataimakin babban hafsan hafsoshi kan harkokin siyasa na shugaban kasar Iran ya ce Bahrain ta aike da sako ga Iran ta hanyar Rasha domin daidaita alaka.

Bahrain ta bi sahun Saudiyya kan yanke huldar diflomasiyya da Iran a ranar 4 ga watan Janairun 2016, bayan da masu zanga-zangar Iran, wadanda suka fusata da hukuncin kisa kan fitaccen malamin Shi’ar nan Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da gwamnatin Saudiyya ta yi, suka kai farmaki kan ofishin jakadancinta da ke Iran.

Amma daga bisani Tehran da Riyadh sun cimma yarjejeniya a birnin Beijing babban birnin kasar Sin a watan Maris din shekarar 2023 inda suka maido da huldar diflomasiya a tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments