Babban kakakin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojinsa ba zasu sake barin makiya su sake tabbatar da ikonsu a yankin yammmacin Asiya ba.
Kamfanin dillancin labaran Mehrnews na kasar Iran ya nakalto Burgedia Janar Abolfadle Shekarchi yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, ‘ba zamu sake barin makiya su sake gina sansanonin sojojinsu ko karfinsi a yankin yammacin asiya ba’.
Ya kara da cewa, dole ne kasashen yankin su fice daga tsarin tsaron da bai da amfani a garesu wanda Amurka ta samar da shi a kasashensu.
Janar Shekarchi ya bayyana cewa Amurka ta koma fasa kori da satar yanya don wucewa da wasu daga danyen man fetur daga mashigar ruwa ta Hurmuz. Sai dai abin tambaya itace wannan zai dore? Idan Amurka ta kasa magance matsalolinta , ta ina zata damu da halin da kasashen yankin suke ciki?
Wani labarin yana cewa, kuna ganin yanda shugaban Amurka ya yi watsi da kasashen turai gaba daya, ya je ya kulla yarjeniya da kasar Rasha don ya samar da makamashi daga ga mutanen Amurka. Idan zai yiwa kasashen turai haka, menene kuke tsammanin makamanku idan al-amura suka dada lalacewa fiye da yanda suke a halin yanzu.
A wani bangare kuma Janar Mohsen Rezaei, ya ce Iran bata amince da martani Trump ga sharuddanta na bude mashigar ruwa Hurmuz ba, inda ya amince da wasu da cikin sharudda 7 wanda Iran ta gabatar mata a MDD. Yace wannan bai wadatar ba.