Iran: Aragchi Ya Zanta Da Tokwarorinsa 12 A Yankin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bada bayanin tattaunawarsa da ministocin harkokin wajen kasashe 12 a yankin a cikin sa’o’ii 48 da suka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bada bayanin tattaunawarsa da ministocin harkokin wajen kasashe 12 a yankin a cikin sa’o’ii 48 da suka gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Asabar, ya kuma kara da cewa, tattaunawar ta kasance kan al-amuran da suka shafi yankin da kuma na kasa da kasa.

Labarin ya kara da cewa ministan ya zanta ta wayar tarho da ministocin harkokin waje na kasashen Oman, Masar, Jordan, Saudi Arabia, Qatar, Cyprus, Türkiya, Kuwait, Hadaddiyar daular larabawa, Tunisia, Iraq da kuma Pakistan.

Yace ya gargadi gwamnatocin Amurka da HKI kan duk wani shirin kaiwa kasar Yaki, da kuma sakamakon hakan.  

Aragchi ya kara da cewa ya bayyana matsayin JMI dangane da mashigar ruwa ta Hurmuz sannan da batun cewa Iran ba zata taba canza matsayinta kan sharuddan da ta bayar tun farko ba. Dole ne Amurka ta cika wadan nan sharudda kafin a fara maganar tattaunawa.

Yace dole ne Amurka ta mutunta kasar Iran da kuma mutanen kasar, ta kawo karshen yakin da ta dorawa kasar, ta kawo karshen shishigi a cikin al-amuran kasashen yankin, ta amince da yencin kasashen yankin na samar da tsarin tsaron yankin ba tare da gayyatarta ba, ko kuma shigarta ba, sannan suna son su zama sune da alhakin kula da tsarin kasashensu.

Daga karshe yace, Iran tana da hakkin kare kasarta daga duk wanda yake son mamayarta.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted