Iran: An Yi Juyayin Cika Shekaru 6 Daga Shahadar Kassim Sulaimani

A jiya Alhamis ne aka yi  taron tunawa da zagayowar cikar shekaru 6 daga shahadar Shahid Kassim Sulaimani anan Tehran wanda ya sami halartar dubban

A jiya Alhamis ne aka yi  taron tunawa da zagayowar cikar shekaru 6 daga shahadar Shahid Kassim Sulaimani anan Tehran wanda ya sami halartar dubban mutane.

Babban masallacin juma’ar Tehran ya cika da mutane da su ka fito daga kowace kusurwa ta birnin domin tunawa da shahid Kassim Sulaimani.

Haka nan kuma taron ya sami halartar manyan jami’an soja da na tsaro da kuma ‘yan siyasa da su ka hada da shugaban kasa.

An gabatar da jawabai da su ka kunshi bayani akan rayuwar shahidin da sadaukar da kansa a fagen fada da ayyukan ta’addancin da Amurka ta kirkira a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.

A jawabin da ya yi, shugaban kasa Mas’ud Pizishkiyan ya ce; Al’ummar Iran za ta ci gaba da tafiya da karfi akan tafarkin Shahid Kassim sulaimani.

Shugaban kasar na Iran ya bayyana Shahid Kassim Sulaimani da cewa abin koyi ne a fagen gwagwarmaya da kare ‘yan’adamtaka, ba a cikin Iran kadai ba, har ma da ko’ina a duniya.

Wannan ne ya sa hatta a cikin Amurka aka sami wadanda su ka yi juyayin shahadarsa, kamar yadda shugaban kasar ta Iran ya bayyana.

Da yake Magana akan makircin Amurka, shugaba kasa Pizishkiyan ya ce abinda Amurka da ‘yan sahayoniya suke yi a wannan lokacin shi ne yi wa masana da jagorori masu son tabbatar da adalci da ‘yanci kisan gilla, alhali su ne manyan masu laifi a duniya.

Shugaban na kasar Iran ya kuma ce,babban dalilin akan cewa Amurka da ‘yan sahayoniya masu aikata laifuka ne shi ne shahadar Kassim Sulaimani da kuma Injiniya Abu Mahdi na Iraki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted