Iran: An Fidda Rahoton Farko Na Kwamintin Bincike Dangane Da Faduwa Jirgin Shugaban Kasa Ibrahim Ra’si

Kwamitin sojoji masu binciken dalilan faduwar jirgin shugaban kasa a ranar Lahadi 19 ga watan mayu da muke ciki ya bada rahotansa na farko dangane

Kwamitin sojoji masu binciken dalilan faduwar jirgin shugaban kasa a ranar Lahadi 19 ga watan mayu da muke ciki ya bada rahotansa na farko dangane da dalilan faduwar jirgin.

Kamfanin dillancin laraban Irna na kasar Iran ya nakalto kwamitin yana fada a rahotonsa na farko kan cewa jirgin ya yi karo na da wani dutse a gangaren tsauni daga tsaunukan yankin da yake wucewa sai ya kama da wuta sannan ya fadi kasa.

Rahoton ya kara da cewa mai yuwa rashin kyawun yani ne ya haddasa faduwar jirgin saboda ruwan sama da kuma tsananin sanyin da ake yi a kan tsaunukan da jirgin yake wucewa. Banda yah aka, yace jirgin bai kaucewa hanyar da aka tsara masa ya bi a wannan tafiyar ba. Banda haka kwamitin yace jami’an tsaro da bada agaji na kasar ne suka gano inda jirgin ya fadi da masalin karfe 5 na safe a ranar litinin 20 ga watan Mayu.

Har’ila yau kwamitin ya kammala da cewa ya zuwa yanzu bai sami wata alama ta harbin albarushi ko wani makami a kan murbushin jirgin da kwamitin ya tattara ba. Kuma babu wani abin kwakwanto ko shakku a maganganun da aka yi tsakanin matukin jirgin da wadanda suke kula ta tafiyarsa na karshe kafin a barjin duriyarsa.

Daga karshe rahoton ya kammala da cewa akwai bayanai da dama da kwamitin ya tattara dangne da faduwar jirgin na shugaban kasa kuma yana bukatar lokaci don duba su cikin nutsuwa.

Kafin haka dai babban hafsan hafsoshin sojojin Iran Janar Muhammad bakiri, kwana guda bayan faduwar jirgin ya bada sanarwan cewa sojojin kasar zasu gudanar da bincike don gano sanadiyyar faduwar jirgin shugaba Ra’isi a kan tsaunukan da ke tsakanin kasar Iran da kuma kasar azarbaijan dake arewa masu yammacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments