Iran: An Bayar Da Lambar Yabo Ta “Imam Khumaini” Ga Wasu Fitattun Mutane A Duniya Da Su Ka Hada Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Na Nigeria

A jiya Laraba ne aka yi bikin kaddamar da kyautar girmamawa mai dauke da sunan: “Imam Khumaini” da ita ce karo na farko ga wasu

A jiya Laraba ne aka yi bikin kaddamar da kyautar girmamawa mai dauke da sunan: “Imam Khumaini” da ita ce karo na farko ga wasu fitattun mutane da su ka yi hidima a bangarori daban-daban ga al’umma.

Daga cikin wadanda su ka karbi kyautar da akwai Ayatullahil-Uzma Abdullahi Jawad Amuli daga Iran, sayyid Abdulmakil Husi daga Yemen da Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky daga Nigeria.

Sheikh Isa Kassim Na Kasar Bahrain ya sami kyautar ne saboda gwagwarmayarsa ta nemawa mutanen kasarsa ‘yanci da kuma kare karama ta bil’adama.

Sai kuma Sheikh Yakubu Ibrahim El-Zakzaky daga Nigeria bisa hidimarsa ga mutane da raunana a wadanda ake zalunta.

Daga kasar Lebanon an mika  lambar  yabon ga sheikh Gazi Haninah saboda yadda  yake fafuta a fagen samar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin musulmi.

Daga kasar Aljeriya an bayar da kyautar ne ga Sheikh Rashid Bin Isa wanda yake yada manufofin Imam Khumaini ( r.a) na farfado da rayuwar addinin musulunci a tsakanin al’umma.

Daga kasar Malysia an bai wa Muhammad Azmi Abdulhamid kyautar yabon ta “Imam Khumain” saboda fada da masu girman kai na duniya da kuma zaluncin ‘yan sahayoniya.

Daga kasar Bosnia an lambar yabon ga malama Mina Moker, sai Sayyidah Fatima Taba’tabai daga Iran saboda aiki da suke yin a yada koyarwar Irfani, da kyawawan halaye.

 Haka nan kuma lambar yabon ta “Imam Khumain” ta shiga hannun Sergey Baburin na kasar Rasha, dake fafutukar ganin adalci ya watsu a duniya haka nan sulhu da zaman lafiya.

Wasu da aka bai wa lambar yabon ta “Imam Khumaini” sun hada Abdullahi Manajit daga kasar Thailand, Yahya fauzi daga Iran saboda bayyana  tunanin ci gaban musulunci da yadda za a sake farfado da shi a wannan zamanin.

  • Shi kuwa Hujjatul-Islam Mahdi Mehrizi ya sami kyautar ne saboda yadda yake yin kira akan daukaka gudunmawar da mata za su rika bayarwa a cikin al’umma da kuma tsarin iyali.

Za a rika bayar da lambar yabon ne dai bayan kodanne shekaru biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted