ICC: Takunkuman Amurka Kan Alkalan Kotun Yin Watine Da Adalacin Kasas  Da Kasa

Kotun hukunta manya-manyan laifuka ta duniya ICC ta bayyana cewa takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin kasar Amurka ta kakabawa wasu alkalan kotun guda biyu kamar

Kotun hukunta manya-manyan laifuka ta duniya ICC ta bayyana cewa takunkuman tattalin arzikin da gwamnatin kasar Amurka ta kakabawa wasu alkalan kotun guda biyu kamar hari ne kan tsarin adalci da gaskiya ta duniya wanda ba dai dai ba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kutun ta ICC tana bada wannan sanarwan a jiya Alhamis ta kuma kara da cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Maco Rubio ne ya bada sanarwan kakabawa alkalan kotun guda biyu takunkuman tattalin arziki, kuma sune mai sharia Gocha Lordkipanidze daga kasar Geogia da kuma mai sharia Eldenebalsuren Damdin daga kasar Mongolia.

Gwamnatin Amurka ta dauki wannan matakin ne don takurawa kotun ta dakatar da bincike kai laifuffukan yakin da yahudawan HKI suka aikata a gaza daga cikin harda Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu da kuma tsohon ministansa na yaki  Yauf Galant. Har’ila yau gwamnatin kasar Amurka ta bukaci kotun ta janye sammacin kama mutanen biyu bisa laifukan yaki da kuma kissan kare dangi da suka aikata a kan Falasdinawa daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 wanda ya zuwa yanzu sun kashe Falasdina akalla dubu 70, kuma har yansun suna ci gaba da kissan.

Gwamnatin kasar  Nerthelands wacce take kotun take da babban cibiyarta a kasar ta yi allawadi da gwamnatin kasar Amurka kan wannan matakin, tare da cewa dole ne kotunan kasa da kasasu gudanar da ayyukansu cikin yenci ba tare da katsalanda na wata kasa ba.

Kafin haka Amurka ta dora irin wadan nan takunkuman na hana jami’an kotun na ICC zuwa Amurka da kuma kwace dukkan kadarorinsu a kasar. Daga ciki har da Karem Khan babban mai gabatar da kara a kotun na ICC. Da kuma yar rahoto na musamman na MDD kan al-amuran Falasdinawa Francesca Albanese.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted