A jiya Laraba ne kotun manyan laifukan da take brinin Hague ta yanke hukuncin zaman kurkuku na shekaru 15 akan tsohon kwamandan rundunar ‘yan tawaye na kasar Afirka ta Tsakiya Mahamat Said Abdel Kani bayan da aka same shi da laifuka akan bil’adama ta hanyar azabtar da fursunoni.
Mai shari’a Miatta Maria Samba ta bayyana halin da fursunoni su ka kasance a kurkukun birnin Bangui da cewa yana cin karo da ‘yan’adamtaka.
Samba ta ce; Da akwai shaidu da su ka bayyana cewa a jikin bangayen kukukun da kawai huji-huji saboda harbe-harbe na bindigogi, da kuma jini. Haka nan kuma ana dukansu da bulala har ta kai suna yin bayan gida da fitsari. Bugu da kari wani daga cikin shaidu ya ce an jefa su a cikin dakin da babu taga suna kwana akan dandamali.
Kungiyar ‘yantawaye ta Seleka ta kwace iko da birnin Bangui na kasar ta Afirka Ta Tsakiya wanda ya yi sanadiyyar guduwar shugaban kasar Farancois Bozize.
Wani da aka cutar da shi a wancan lokacin mai suna Poussinga ya ce; A Yau zan yi bacci da saleba saboda kotu ta amince da wahalhalun da na shiga.
A cikin watan Yuli na shekarar da ta gabata 2025 an hukunta wasu mutane biyu ‘ya’yan kungiyar “Anti Balaka” wacce ita ma ta ‘yan tawaye ce wacce ta yi fada da kungiyar Seleka.