Hukumar Abinci Ta Duniya FAO Ta Bawa Kasar Iran Lambar Yabo Ta Kula Da Kasar Noma

Kasar Iran ta karbi lambar yabo kan kula da kasar noma a wani biki wanda hukumar abinci ta Duniya FAO ta shirya a kasar Thailand

Kasar Iran ta karbi lambar yabo kan kula da kasar noma a wani biki wanda hukumar abinci ta Duniya FAO ta shirya a kasar Thailand a ranar Alhamis da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa mataimakin minista a ma’aikatar noma ruwa da kasa ne ya karbi lambara yabon da kansa a inda ake gudanar da bukukuwan a kasar Thailan.

Sarkin kasar Thailanda yake bada wannan yabon kuma kasar Iran ce ta shirya bikin ranar ruwa da kasa ta duniya a shekara ta 2023 da ta gabata.

Labarin ya kara da cewa gwamnatin kasar Rasha ta bada wani kyauta ga kasar ta Thaiwan saboda ayyukan da ta gabatar a bangaren gyaran kasar noma.

Mataimakin ministan noma na kasar Iran a taron na ranmar kasar noma da ruwa ta duniya, ya gabatar da jawabin a taron na Thailand inda ya godewa wadanda suka shirya taron ya kuma bayyana muhimman kula da kasar noma da kuma ruwa saboda ayyukan noma a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments