Iran: PGSA Ta Sanya Jiragen Ruwa 122 Cikin Masu Aikata Laifi

Hukuma mai kula da mashigar ruwa ta Hurmuz a nan Iran wato (PGSA) ta bada sanarwan sanya jiragen ruwa 122 cikin jerin wadanda suka sabawa

Hukuma mai kula da mashigar ruwa ta Hurmuz a nan Iran wato (PGSA) ta bada sanarwan sanya jiragen ruwa 122 cikin jerin wadanda suka sabawa dokokin hukumar kuma tuni ta dau mataki a kan 40 da cikinsu a yayin da wasu kimani 30 suna tattaunawa da hukumar don kada a sanysu cikin jirin sunayen ko kuma a ciresu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shafin yanar gizo na hukumar yana bayanin hakan ya kuma kara dacewa.

Labarin ya kara da cewa jirage guda biyu sun amince su gyara halinsu don kada a sanyasu cikin jerin sunayen jirage masu sabawa dokokin hukumar. Daga karshe bayanin ya kara da cewa, mai yuwa a kara sunayen jiragen ruwa 30 wadanda ake bincike a kansu.

Hukumar tana iya hana wasu jirage wucewa da mashigar ruwan idan taga laifinsu ya kai hakan ko kuma a hanasu wucewa na wani lokaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted