Rahotannin da suke fitowa daga kasar Siriya sun bayyana cewa, mayakan hai’at Tahrir Asham, tana fafatawa da kananan kungiyoyi dauke da makamai, mafi yawansu a gruruwan bakin ruwa na kasar, inda ake bada rahoton kisa tashin hankali, wuwuran kayakin jama’a, garkuwa da mutane da sauransu a ko wani minti 10.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana HTS tana kokarin hada dukkan kungiyoyin da suka taimaka don kifar da gwamnatin Bashar Al-Asad, saboda su mika makamansu don dawo da zaman lafiya a kasar.
Sai dai kimani wata guda guda Kenan da kifar da gwamnatin Asad amma tashe –tashen hankula sai kara yawa suke a akasar.
Shugaban Muhammad Julani, ya gana da shuwagabannin kungiyoyi daban-daban inda ya bukaci su tattara makamansu don tabbatar da zaman lafiya a kasar