Ragowar ministocin jam’iyyar New Social Contract na Netherland sun yi murabus daga gwamnati, jim kadan bayan da ministan harkokin wajen kasar Kasper Voldkamp ya sanar da murabus dinsa a ranar Juma’a, sakamakon dakile daukar matakai masu tsauri kan mamayar Isra’ila da kuma ayyukan yakin da take tafkawa a Gaza da gabar yammain Kogin Jordan a kan Falastinawa.
Karin Ministocin da suka yi murabus sune: Ministan Harkokin Jama’a Eddie van Heum, Ministan Harkokin Cikin Gida Judith Ottermark, Ministan Ilimi Ebbo Bruins, da Ministan Lafiya Daniel Jansen, baya ga wasu kananan ministoci hudu.
Tare da ficewar dukkanin Ministocin jam’iyyar New Social Contract daga gwamnati, hadakar da ta kafa gwamnati ta rushe, a halin yanzu sai gwamnatin wucin gadi kafin kafa wata sabuwar gwamnati ta daban.
A mayar da martani, firaministan kasar Holland Dick Schoof ya ce “zai nemi shawara kafin ya yanke shawarar yadda za a ci gaba” da tafiyar gwamnatin, bayan murabus din adadi mai yawa na ministocinsa.